Kasashen Nigeria Da Faransa sun Karfafa Yerjejeniyar Tsaro A Tsakaninsu
Gwamnatocin Nigeria da Faransa sun kara karfafa dankon zumunci a tsakaninsu a yau Alhamis.
Gwamnatocin Nigeria da Faransa sun kara karfafa dankon zumunci a tsakaninsu a yau Alhamis. Shafin yanar gizo na labarai Africatime ya ya bayyana cewa ministan harkokin tsaro na kasar Faransa Jean-Yves Le Drian da tokoransa na tarayyar Nigeria Mansur Dan Ali ne suka sanya hanu a kan takardun kara dankon zumuncin, wanda ya hada da na bangaren tsaro da yakar kungiyar Boko Haram. Kasashen biyu suna aiki tare a bangaren tsaro tun cikin watan Decemban shekara ta 2014 a bangaren bayanan sirri kan kungiyar Boko Haram.
Ministan tsaron kasar ta Faransa ya kara da cewa babbar damuwarsa shi ne samun hadin kai don yakar kungiyar boko Haram a yankin.
Kasashen Chadi, Niger da Kuma Kamaru dukkaninsu makobta ga tarayar Nigeria tsoffin kasashen da Faransa ta yiwa mulkin mallaka ne, kuma haryanzun tana da karfin fada a ji a kasashen.
A baya dai gwamnatin kasar Faransa ta tallafawa Nigeria ta bayanin sirri daga hotunan da jiragen leken asirinta da suke birnin Njamaina na kasar chadi suka dauka a yankunan da kungiyar Boko Haram take iko da su a lokacin a arewa masu gabacin kasar ta Nigeria.