Burkina Faso : An Soke Sammacin Kame Compaore Da Guillaume Soro
Kotun karya shari'a a Burkina Fasa, ta soke sammacin kasa da kasa na kotun sojin kasar kan kame tsohon shugaban kasar Blaise Compaore da kuma kakakin majalisar dokokin kasar Ivory Coast Guillaume Soro.
A cewar babban mai shiga da kara na kotun, Armand Ouédraogo an soke dukkannin sammacin ne saboda ba'a bi hanyoyin da suka da dace ba, wanda a cewar sa ko da yaushe idan aka gyara su za'a iya fitar da sammacin.
A ranar 4 ga watan Oktoba bara ne kotun sojin burkina faso ta fitar da sammacin kame Mr Compaore dake gudun hijira a kasar Ivory Coast tun bayan zanga-zangar al'ummar kasar data yi awan gaba da mulkin sa a ranar 31 gatan Oktoba 2014.
Ana dai zargin Mr Compaore da hannu a kisan da akayi wa tsohon shugaban kasar Thomas Sankara a yayin juyin mulkin 15 ga watan Oktoba 1987.
kazalika kotun sojin kasar na zargin Mr Guillaume Soro kakakin majalisar dokokin kasar Ivory Coast da hannu a yunkurin juyin mulkin da baiyi nasara ba kan gwamnatin rikon kwarya ta Burkina Faso a watan Satumba bara.