Bankin Duniya Ya Dakatar Da Bada Rance Ga Mozambique
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i4519-bankin_duniya_ya_dakatar_da_bada_rance_ga_mozambique
Bankin duniya ya sanar da dakatar da bada wasu rancensa ga kasar Mozambique, bayan gano wani bashin boye na kimanin $ Biliyan 1,4 da kasar ta yi.
(last modified 2018-08-22T06:58:12+00:00 )
Apr 29, 2016 00:00 UTC
  • Bankin Duniya Ya Dakatar Da Bada Rance Ga Mozambique

Bankin duniya ya sanar da dakatar da bada wasu rancensa ga kasar Mozambique, bayan gano wani bashin boye na kimanin $ Biliyan 1,4 da kasar ta yi.

Abokan hulda kasar dai sun ce basu gamsu ba ko kadan da boye bashin da kasar ta Mozambique tayi ba.

Wannan dai na zuwa ne bayan da asusun bada lamuni na duniya wato IMF shi ma ya dau matakin dakatar da bada rancensa ga kasar a tsakiyyar Wannan wata na Afrilu da muke ciki.

Wani kakakin bankin ya ce nan gaba zasu san matakin da zasu dauka kan kasar ta Mozambique.

A ranar Talata data gabata hukumomin na Maputo a karaon farko sun fito sunyi bayyani kan rancen kudaden, wanne a cewar akayi amfani dasu wajen kafa wani sansanin sojin ruwa, saidai ba tare da yin bayyani dalla-dalla ba kan yadda aka kashe kudaden.