Laberia : George Weah, Zai Tsaya Takara A Zaben Shugaban kasa
-
Tsohon dan wasan tamola na kasa da kasa, kana dan adawa a Laberia, George Weah
Tsohon dan wasan tamola na kasa da kasa, kana dan adawa a Laberia, George Weah ya yi alkawarin lashe zaben shugaban kasar na 2017 da ya sanar da shiga takara sa a hukumance jiya Alhamis.
George Weah, ya bayyana hakan ne gaban dubban magoya bayan sa na jam'iyyar CDC cewa, bayan la'akari da korafe-korafe su zai tsayawa takara a zaben kasar na badi.
Dan shekaru 49 a duniya, George Weah wadan shi ne wani dan wasan tamola na nahiyar Afrika daya taba samun kwallon zinare, dama ya taba fafatawa da shugabar kasar Ellen Johnson Sirleaf a zaben 2005, kafin daga bisani ya sake tsayawa takara a 2011 a matsayin dan takara mataimakin shugaban kasar.
kasancewar a wannan karo, Mme Sirleaf ba zata tsayawa takara ba saboda kundin tsarin mulkin kasar ya hana mata haka, George Weah zai fafata da mataimakin ta Joseph Boakai, dan shekaru 71 a duniya.