Najeriya : Jaddada Alkawalin Murkushe Kungiyar Ta'addanci Ta Boko haram
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i4531-najeriya_jaddada_alkawalin_murkushe_kungiyar_ta'addanci_ta_boko_haram
Jaddada Alkawalin Murkushe Kungiyar Ta'addanci Ta Bokoharam
(last modified 2018-08-22T06:58:12+00:00 )
Apr 29, 2016 07:52 UTC
  • Najeriya : Jaddada Alkawalin Murkushe Kungiyar Ta'addanci Ta Boko haram

Jaddada Alkawalin Murkushe Kungiyar Ta'addanci Ta Bokoharam

Shugaban Kasar Najeriya Muhammad Buhari ya jaddada aniyar gwamnatin kasarsa ta murkushe Bokoharam.

Kamfanin dillancin labarin Xinhua na kasar Sin ya ambato shugaban na kasar Najeriya Muhammad Buhari yana fada a yau juma'a cewa; gwamnatin kasar a shirye ta ke, ta kare dukkanin fadin kasar daga barazanar bokoharam.

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana haka ne a ganawarsa da ministan tsaron kasar faransa Jean-Yves Le Drian a yau juma'a.

A jiya alhamis ma dai an yi wata ganawar a tsakanin ministan tsaron kasar ta Faransa da kuma takwaransa na Najeriya Mansur Dan Ali. Dukkanin bangarorin biyu dai sun sha alwashin fada da kungiyar 'yan ta'addar ta bokoharam