Sudan Ta Kudu : Kafa Majalisar Ministoci Ta Hadaka
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i4537-sudan_ta_kudu_kafa_majalisar_ministoci_ta_hadaka
Kafa Majalisar Ministoci Ta Hadaka
(last modified 2018-08-22T06:58:12+00:00 )
Apr 29, 2016 07:53 UTC
  • Sudan Ta Kudu : Kafa Majalisar Ministoci Ta Hadaka

Kafa Majalisar Ministoci Ta Hadaka

Shugaban Kasar Sudan ta kudu ya bada umarnin kafa majalisar hadin kan kasa.

Jaridar Kasar Masar ta al-Yaumu Sabi'i ta ambaci cewa; Shugaba Silva Kiir na kasar Sudan ta kudu ya bada umrnin da a shigar da 'yan tawayen kasar da kaso 1%3 a cikin majalisar ministocin kasar mai mambobi 30.

Matakin na shugaba Kiir dai ya zo ne bayan watanni da cimma yarjejeniyar kaa gwamnatin hadin kan kasa da gwamnati da kuma 'yan tawaye karkashin Reikh Machar su ka cimmawa.

Kasar Sudan ta kudu ta fada cikin tashin hankali ne saboda sabani da ya kunno kai a tsakanin shugaba Silva Kiir da mataikaminsa Reikh Machar da ya sauke daga kan mukamin nashi.