Wasu 'Yan Bindiga Sun Kai Hari Kan Sansanin Sojin Jamhuriyar DR Congo
Wasu gungun mahara sun kai farmaki kan sansanin sojin gwamnatin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo, inda suka halaka soja guda tare da jikkata wasu adadi na daban.
Shafin watsa labaran Afrika Time ya watsa rahoton cewa: Wasu gungun mahara da ba a san ko su wane ne ba sun kaddamar da harin wuce gona da iri kan sansanin sojin gwamnatin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo da ke kauyen Mulamba a yankin Masisi a lardin Kivu ta Arewa a jiya Alhamis, inda suka kashe soja guda tare da jikkata wasu uku na daban.
Wata majiya a yankin ta bayyana cewa; Ana zargin 'yan kungiyar Nyatura da suke goyon bayan kungiyar 'yan tawayen kasar Ruwanda na kungiyar "FDLR" da hannu a kai harin, amma mahukuntan kasar suna ci gaba da gudanar da bincike domin zakulo maharan.