Wani sabon Rikici ya kunno kai tsakanin 'yan tawaye da Sojojin Sudan
Wani sabon Rikici ya barke tsakanin Sojojin Sudan da 'yan tawaye a yankin Kurdufan ta Kudu.
Kamfanin dillancin Labaran Kasar Faransa ya nakalto Arnu Lodi kakakin 'yan tawayen yankin na Kurfadan a yau Assabar na cewa gumurzu tsakaninsu da Dakarun tsaron Gwamnati ya yi sanadiyar mutuwar mayakan su 6 tare da jikkata wani adadi mai yawa daga cikinsu.Wannan dai shine sabon rikici da ya barke tsakanin bangarorin biyu tun bayan wata guda da ya gabata.
A nasu bangare Dakarun tsaron Gwamnati sun tabbatar da cewa rikici ya barke ne a ranar Larabar da ta gabata a garin Oum Sediba.
Tun daga shekarar 2011 zuwa yanzu Dakarun tsaron Sudan ke yakar 'yan tawaye a yankunan Kurdufan ta kudu da Blue Nil.
A karshen shekarar 2015, Shugaban Kasar Sudan Umar Albashir ya shelanta dokar tsagaita wuta a wadannan yankuna, sannan wata guda da ya gabata ya sake sabunta wannan doka.
Alkaluma sun bayyana cewa rikicin kudancin Sudan din ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama sannan kuma ya raba wasu sama da million biyu da mahalinsu.