Sudan : Sojoji Biyar Suka Mutu A Hadarin Jirgin Soji
May 01, 2016 01:21 UTC
-
hadarin wani jirgin sama
Rindinar sojin Sudan ta ce sojojin ta biyar ne suka mutu a hadarin wani jirgin sama soji a yankin Kurdofan dake arewacin kasar.
Jirgin dai yayi hadari ne jiya Asabar, sakamakon matsala da ya samu wajen sauka a filin jiragen saman na El-Obeid.
Sanarwar rindinar sojin ta ce dukkannin mambobin jirgin biyar wanda suka hada da ofisa uku da sojoji biyu.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da wani sabon Rikici ya barke tsakanin Sojojin Sudan da 'yan tawaye a yankin Kurdufan ta Kudu, wanda ya yi sanadiyar mutuwar 'yan tawaye 6 tare da jikkata wani adadi mai yawa.
Wannan dai shi ne sabon rikici da ya barke tsakanin bangarorin biyu tun bayan wata guda da ya gabata.
Tags