Damuwar Kungiyar FAO kan yanayin 'yan gudun hijrar Najeriya
Kungiyar samar da Abinci ta Duniya wato Fao ta bayyana damuwarta kan halin da duban 'yan gudun hijra ke ciki a Najeriya
Kamfanin dillancin Labaran Kasar Faransa daga birnin Geneva ya habarta cewa A jiya Lahadi, Kungiyar Samar da abinci ta Duniya FAO ta bayyana damuwarta kan halin da 'yan gudun hijra da hare-haren kungiyar boko haram ya bara da mahalin su ke ciki a Tarayyar Najeria.
Kungiyar Ta FAO ta bayyana cewa Miliyoyin 'yan gudun hijra ne ke fuskantar barazanar mutuwa saboda rashin abin za su ci, inda rahotanni ke cewa wasunsu ma sai sun tona gidan tururuwa domin samun abinci da za su sarrafa su ci.kuma wannan lamari babban tashin hankali ne.
Alkaluma sun ce kashi 10 cikin 100 kacal na 'yan gudun hijrar da adadinsu ya haura million biyu ke samun kulawa a sansanin 'yan gudun hijrar.