An kwato Yankuna da dama daga hanun kungiyar Ashabab a Somaliya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i4636-an_kwato_yankuna_da_dama_daga_hanun_kungiyar_ashabab_a_somaliya
Kungiyar Tarayyar Afirka da Somliya Sun sanar da kwato yankuna da dama daga Hanun kungiyar Ashabab a kasar Samaliya.
(last modified 2018-08-22T06:58:12+00:00 )
May 02, 2016 02:26 UTC
  • An kwato Yankuna da dama daga hanun kungiyar Ashabab a Somaliya

Kungiyar Tarayyar Afirka da Somliya Sun sanar da kwato yankuna da dama daga Hanun kungiyar Ashabab a kasar Samaliya.

A wata Sanarwa da ya fitar Mista Da'ud Haji Iro Kakakin Jihar Middle Shabelle dake tsakiyar Somaliya ya ce Dakarun tsaron kasar tare da taimakon na Kungiyar Tarayyar Afirka sun samu nasarar 'yanto yankunan Runir-dieu,De Nur-dugle da D'ad adeyles dake cikin jihar.

Da'ud Haji Iro ya ce wannan nasara da Dakarun tsaron suka samu ya biyo bayan farmakin da suke kaiwa ne ba dare ba rana kan mayakan Ashabab da kuma hakan ya dawo da konciyar hankali gami da tsaro a Jihar ta Middle Shabelle.

Da'ud Haji Iro ya tabbatar da cewa A yayin 'yanto wadannan yankuna babu wani farar hula da ya rasa ransa kuma suna kyautata fatan cewa nan dan lokaci Dakarun tsaro na Kungiyar Tarayyar Afirka su kwato sauren yankunan da suka rage a hanun Kungiyar ta Ashabab.

Tun a shekarar 2007 aka kafa Dakarun tsaron Kasashen Afirkan dake kasar Somaliyan wato AMUSMA da suka gumshi Sojojin kasashen Kenya, Habasha, Uganda da Burundu,kuma ya zuwa yanzu sun samu nasarar sosai a yakin da suke yi tare da kungiyar ta'addancin nan ta Ashabab, inda suka kwato jihohi da yankuna da dama a kasar.