RD Congo Ta Lashe Gasar CHAN 2016
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i466-rd_congo_ta_lashe_gasar_chan_2016
Congo ta Lallasa Mali da Ci 3 - 0
(last modified 2018-08-22T06:57:47+00:00 )
Feb 08, 2016 02:49 UTC
  • Taswurar Afirka
    Taswurar Afirka

Congo ta Lallasa Mali da Ci 3 - 0

Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo ta dauki kofin gasar nahiyar Afirka ta 'yan gida wato CHAN, bayan da ta lallasa Mali da ci 3-0, a wasan karshe, da yammacin jiyya Lahadi a Kigali babban birnin kasar Rwanda.

Dan wasan Congo, Meshack ne dai ya fara jefa kwallon farko a ragar ta Mali, minti 29 da fara wasa. Meshack din ne dai ya kuma kara ta biyu. Jonathan Bolingi ne ya zura ta uku.

Wannan dai shi ne karo na biyu da DR Congon take lashe kofin gasar wadda aka fara a 2009.

A 2009 ta dauki kofin bayan da ta doke Ghana da ci 2-0.