Samamcin Kasa Da Kasa Na Kamo Tsohon shugaban kasar Borkina Faso
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i4672-samamcin_kasa_da_kasa_na_kamo_tsohon_shugaban_kasar_borkina_faso
An fitar da sammacin kasa da kasa domin taso keyar tsohon shugaban kasar Blaise Compaore zuwa gida.
(last modified 2018-08-22T06:58:13+00:00 )
May 02, 2016 14:30 UTC
  • Samamcin Kasa Da Kasa Na  Kamo Tsohon shugaban kasar Borkina Faso

An fitar da sammacin kasa da kasa domin taso keyar tsohon shugaban kasar Blaise Compaore zuwa gida.

Majiyar watsa labaru ta Africa Taime ta ambato majiyar kotun sojan kasar Borkina Faso tana cewa;An fitar da sammacin kasa da kasa domin taso keyar tsohon shugaban kasar Blaise Compaore zuwa gida.

Dama dai tun da fari babban mai shigar da kara na soja a birnin Ougadugu Nobert Koudougou ya sanar da cea ba ya ga tsohon shugaban kasar da za a kamo za kuma a taso keyar tsohon shugaban Majalisar dokokin Guillaume Soro.

A cikin watan Decemba na 2015 aka fara tuhumar Blaise Compaore da ya ke gudun hijira a kasar Cote De Voire, da cewa yana da hannu wajen kashe shugaba Thomas Sankara.