Najeriya : An Karkata $ Biliyan 15 Na Sayan Makamai A Gwamnatin Data Gabata
-
Mataimakin shugaban Najeriya, Yemi Osinbajo
Mataimakin shugaban Najeriya, Yemi Osinbajo ya zargi gwamnatin kasar data gabata da karkata akalan wasu kudade da aka ware domin sayan makaman da yawan su ya kai Dallar Amurka Biliyan 15.
Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana haka ne a wani taron biki da ya halarta a jami’ar Ibadan da ke jihar Oyo a cewar wata sanarwa daga ofishin sa, kamar yadda kanfanin dilancin labaren faransa na AFP ya rawaito.
Makuden kudaden da ake zargin tsafin jami'an gwamnatin wacen lokacin ta Goodluck Jonathan da wawushewa yawansu ya kai kimanin rabin abinda ke cikin asusun waje na Najeriya.
Gwamnatin shugaban kasar dai Muhammadu Buhari ta ce ba za ta kyale duk wani jami’in da aka samu da hannu a cin hanci da rashawa ba, kamar yadda tayi alkawari.
Cin hanci da karbar rashawa na daya daga cikin al'amuran dake zamen karfe kafa ga tattalin arzikin wannan kasa dake a matsayin ta farko a Nahiyar Afirka.