An cabke 'yan ta'adda Uku a kasar Kenya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i4756-an_cabke_'yan_ta'adda_uku_a_kasar_kenya
Kwamandan 'yan sandar kenya ya sanar da kame wasu Mutane uku da ake zarkin 'yan ta'addar ISIS ne a yankin Wet dake kudu maso gabashin Nairobi babban birnin Kasar.
(last modified 2018-08-22T06:58:13+00:00 )
May 04, 2016 11:02 UTC
  • An cabke 'yan ta'adda Uku a kasar Kenya

Kwamandan 'yan sandar kenya ya sanar da kame wasu Mutane uku da ake zarkin 'yan ta'addar ISIS ne a yankin Wet dake kudu maso gabashin Nairobi babban birnin Kasar.

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya nakalto babban Kwamandan 'yan sandar kenya a yau Laraba na cewa sun kame mutanan ne a yayin da suke kokarin kai wani hari na ta'addanci a kasar, daga cikin mutane ukun da aka kame har da wani dalibin Jami'a na koyon aikin Likita kuma tuni aka fara gudanar da bincike a kansu.

Kwamnandan ya ce Kungiyar ta ISIS na iya kokari wajen jan hankalin Daliban jami'ar kasar, har lokacin da za su fada cikin tarkonta su dinga kai hare-haren ta'addanci a cikin kasar.

A nasu bangare jami'an 'yan sandar dake yaki da ta'addanci sun samu nasarar gano tare da rusa wata kafar yanar gizo a tsakanin dalibai wacce ke kiran su zuwa jihadi a kasar Libiya da Gabas ta tsakiya.

Tun daga shekarar 1998, kasar ta farar fuskantar hare-haren 'yan ta'adda.