Shugaban Murtaniyya Ya Bukaci A Rusa Majalisar Dattawan Kasar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i4777-shugaban_murtaniyya_ya_bukaci_a_rusa_majalisar_dattawan_kasar
Shugaban kasar Mauritaniya Mohamed Ould Abdel Aziz yayi kiran da a rusa majalisar dattawan kasar yana mai cewa majalisar ba ta da wani amfani ko kuma in ma tana da shi to dan kadan ne.
(last modified 2018-08-22T06:58:13+00:00 )
May 05, 2016 01:00 UTC
  • Shugaban Murtaniyya Ya Bukaci A Rusa Majalisar Dattawan Kasar

Shugaban kasar Mauritaniya Mohamed Ould Abdel Aziz yayi kiran da a rusa majalisar dattawan kasar yana mai cewa majalisar ba ta da wani amfani ko kuma in ma tana da shi to dan kadan ne.

Shugaba Mohamed Ould Abdel Aziz ya bayyana haka ne a wani jawabi da yayi a garin Nema, da ke gabashin kasar inda ya ce amfanin majalisar dai kadan ne in ma akwai kenan, don haka ya kara da cewa nan gaba kadan za a gabatar da wani kuduri na yin kwaskwarima ga kundin tsarin mulkin kasar a wannan kasar da kuma gudanar da kuri'ar jin ra'ayin al'umma kan wannan lamarin.

Har ila yau shugaban ya kirayi 'yan adawan kasar da su shigo cikin kuri'ar raba gardamar yana mai ba su wa'adin makonni uku zuwa hudu na su shigo din.

Shugaba Abdel'aziz ya zargin 'yan majalisar mai membobi 58 da saibi wajen kada doka a kasar lamarin da a cewarsa ke barazana ga ci gaban kasar.

'Yan adawa da kungiyoyin kare hakkokin bil'adama suna zargin shugaban Murtaniyyan da shirin ci gaba da zarce bayan wa'adin mulkinsa ya kare a shekara ta 2019, bayan da wasu daga cikin 'yan majalisar ministocinsa suka fara kiran da a yi kwaskwarima ga kundin tsarin mulkin kasar don ba shi damar sake tsayawa a kan karagar mulkin kasar.