Tsananta kai hare-hare kan 'yan tawayen Uganda A gabashin D/Congo
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i4834-tsananta_kai_hare_hare_kan_'yan_tawayen_uganda_a_gabashin_d_congo
Mataimakin Kwamandan Dakarun sulhu na MDD a Kasar D/Congo ya sanar da tsananta kai farmaki kan 'yan tawayen Uganda a gabashin kasar
(last modified 2018-08-22T06:58:14+00:00 )
May 06, 2016 06:34 UTC
  • Tsananta kai hare-hare kan 'yan tawayen Uganda A gabashin D/Congo

Mataimakin Kwamandan Dakarun sulhu na MDD a Kasar D/Congo ya sanar da tsananta kai farmaki kan 'yan tawayen Uganda a gabashin kasar

Janar Jean Baillaud ya ce Dakarun Tsaro da Sulhu na majalisar Dinkin Duniya za kara kai yawan farmakin da suke kaiwa kan 'yan tawayen Uganda dake gabashin Congo.

Ana dai zarkin 'yan tawayen na Uganda da kai hare-hare kan fararen hula A yankin Beni dake jihar Kivo ta arewa na arewacin D/Congo.

Bayan Rahotani na kisan Fararen hula 17 da 'yan tawayen na Uganda suka yi a anguwar Bangachu-luna dake yankin na Beni, Mataimakin Kwamandar Dakarun sulhun na MDD ya isa gurin da wannan lamari ya auku inda ya gudanar da bincike.

A cikin rahoton farko da ya gabatar ya tabbatar, ya ce Mata da Kananen yara na daga cikin wadanda 'yan tawagen na Uganda suka yi wa kisan gilla.

Tun shekaru 20 da suka gabata, gabashin kasar D/Congon ke fuskantar matsalar tashin hankali sakamakon hare-haren 'yan tawayen Uganada.