Amurka Za ta Sayarwa da Najeriya Jiragen yaki
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i4837-amurka_za_ta_sayarwa_da_najeriya_jiragen_yaki
Amurka ta bada labarin aniyarta ta sayar wa da kasar Najeriya jiragen yaki
(last modified 2018-08-22T06:58:14+00:00 )
May 06, 2016 14:17 UTC
  • Amurka Za ta Sayarwa da Najeriya Jiragen yaki

Amurka ta bada labarin aniyarta ta sayar wa da kasar Najeriya jiragen yaki

Kamfanin Dillancin Labarun Reuters ya ambato wata majiyar sojan Amurka tana cewa; A halin da ake ciki, Amurkan tana nazari da bincike akan sayarwa da najeriya jiragen yaki 12 samfurin A-29 Super Tunaco domin fada da kungiyar bokoharam.

Gwamnatin ta Amurka tana kuma yin wani nazarin sayarwa da Najeriyan wasu kayan yaki da ake amfani da su wajen bin diddigin abokan gaba, haka nan kuma bada horo ga sojojin da za su yi amfani da su.

Majiyar Amurkan ta ce; sayarwa da Najeriya makamai a wanann lokacin yana nuni da yadda gwamnatin Amurkan ta aminta da shugaba Muhammadu Buhari, sabanin tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan da Amurkan ta kakabawa takunkumin makamai.