CRA : Abdul. Karim Mekassoua Na Unguwar Musulmi Ya Zama Kakakin Majalisa
May 07, 2016 01:21 UTC
-
sabon kakakin majalisa Afirka ta tsakiya, Abdul karim Meckassoua
Yan majalisar dokoki a jamhuriya Afirka ta tsakiya sun zami tsohin ministan kasar na unguwar musulmi ta PK5 a matsayin kakakin majalisar dokokin kasar.
A cikin 'yan takara bakwai da suka nemi kujera, Mr Abdul Karin ya samu kuri'u 65 na 'yan majalisu 127 da suka kada kuri'a.
Daga cikin wadanda suka nemi shugabancin majalisar har da Anicet Georges Dologuélé daya sha kaye a zagaye na biyu na zaben shugaban kasar.
Abdoul Karim Meckassoua dan shekaru 62 a duniya ya taba kasancewa tsohon minista a lokacin tsohuwar gwamnatin da Mr Touadéra dake shugabancin kasar a yau yake rike da mukamin firaminista a lokacin tsohon shugaba François Bozizé.
Tags