Harin ta'addanci ya hallaka jami'an 'yan sanda biyu a kasar Somaliya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i4978-harin_ta'addanci_ya_hallaka_jami'an_'yan_sanda_biyu_a_kasar_somaliya
Wasu Jami'an 'yan sandan Somaliya biyu sun hallaka sanadiyar tashin Bom a birnin Magadushu.
(last modified 2018-08-22T06:58:15+00:00 )
May 09, 2016 05:51 UTC
  • Harin ta'addanci ya hallaka jami'an 'yan sanda biyu a kasar Somaliya

Wasu Jami'an 'yan sandan Somaliya biyu sun hallaka sanadiyar tashin Bom a birnin Magadushu.

Kamfanin dillanin Labaran Reuteus ya nakalto Muhamad Noor jami'in 'yan sandar birnin Magadushu a yau Litinin na cewa sanadiyar tashin wata mota shake da bama-bamai a hedkwatar 'yan sandar dake kula da zirga-zirga a birnin Magadushu, 'yan sanda biyu sun rasa rayukansu yayin da wasu uku na daban suka jikkata.

Muhamad Noor ya ce wannan harin ta'addancin na motar bama-bamai, an kai shi ne da nufin rushe ginin ma'aikatar, sannan kuma Jami'an 'yan sandar sun bindige daga daga cikin maharan har lahira a yayin da yayi kokarin kutsaya cikin ginin.

A cewar mazunar anguwan, bashewar bama-baman ta yi sanadiyar rushewar gaban ginin ma'aikatar kuma ya janyo asara mai yawa ga shagunan dake makobtaka da hedkwatar 'yan sandar.

Tuni dai kungiyar ta'addancin nan ta Ashabab mai alaka kut da kut da alka'ida ta dauki alhakin harin.