Ruwanda : Zabtarewar Kasa Ta Kashe Mutane 49
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i4984-ruwanda_zabtarewar_kasa_ta_kashe_mutane_49
Hukumomi a kasar Ruwanda sun ce akalla mutane 49 ne suka rasa rayukan su sakamakon zabtarewa kasa da aka fuskanta biyo bayan tafka ruwan sama kamar da bakin kwarya.
(last modified 2018-08-22T06:58:15+00:00 )
May 09, 2016 11:19 UTC
  • zaftarewar kasa a Ruwanda
    zaftarewar kasa a Ruwanda

Hukumomi a kasar Ruwanda sun ce akalla mutane 49 ne suka rasa rayukan su sakamakon zabtarewa kasa da aka fuskanta biyo bayan tafka ruwan sama kamar da bakin kwarya.

Wata sanarwa da gwamnatin kasar ta fitar ta ce lamarin ya auku ne a karshen makon jiya a wasu sassan kasar hudu lamarin da yayi sanadin rasa rayukan jama'a da dama da kuma hasara dukiya mai yawa.

Lamarin dai a cewar sanarwar yafi kamari a Lardin Gakenke dake arewacin kasar inda mutane 34 suka rasa rayukan, sauran lardinan da lamarin ya auku sun hada da Muhanga, Rubavu da kuma Ngororero dake yammacin kasar.

Bayanai sun nuna gidaje sama da 500 ne suka rushe, kana hanyoyi da dama sun lalace.

A cikin wannan shekarar kawai mutane 67 suka mutu, yayin da gidaje sama da 1, 500 suka rushe.