Najeriya : Kotu Ta Goyi Bayan Daurin Shekaru 25 Ga 'Yan Boko Haram
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i4987-najeriya_kotu_ta_goyi_bayan_daurin_shekaru_25_ga_'yan_boko_haram
Kotun daukaka kara a birnin Legas a tarayyar Najeriya ta goyi bayan hukuncin daurin shekaru 25 ga wasu mutane uku da ake zargin alakarsu da kungiyar Boko Haram.
(last modified 2018-08-22T06:58:15+00:00 )
May 09, 2016 12:15 UTC
  • Najeriya : Kotu Ta Goyi Bayan Daurin Shekaru 25 Ga 'Yan Boko Haram

Kotun daukaka kara a birnin Legas a tarayyar Najeriya ta goyi bayan hukuncin daurin shekaru 25 ga wasu mutane uku da ake zargin alakarsu da kungiyar Boko Haram.

Wata sanarwa da gwamnatin Legas ta fitar ta ce, mai shari’a Ibrahim Buba ne ya tabbatar da goyon bayan hukuncin wanda babbar kotun tarayya ta yanke a cikin watan Satumba shekara ta 2014.

Bayani sun nuna cewa yanke wannan hukuncin ne a asirce saboda dalilai na tsaro, duk da yake kungiyoyin kare hakkin bil adama sun so a gudanar da shi a bainar jama’a.

Kotun dai ta samu Ali Muhammad Madu da Adamu Ali Karumi da Ibrahim Usman Ali da laifin ta’addanci da mallakar makaman yaki bayan an tuhume su a watan Maris na shekarar 2013.

Rikicin kungiyar Boko Haram wanda ya fi tsananta a yankin arewa maso gabashin Najeriya, ya kashe mutane akalla dubu 20 yayin da kusan miliyan 3 suka rasa muhallansu.