Sojojin Gwamnatin Nigeriya Suna Ci Gaba Da Kokarin Tsarkake Dajin Sambisa
Rundunar sojin Nigeriya tana ci gaba da samun nasara a kokarin da take yi na tsarkake dajin Sambisa daga 'yan kungiyar Boko Haram a kasar.
Kakakin rundunar sojin Nigeriya Kanal Sani Usman ya sanar da cewa: Sojojin gwamnatin Nigeriya suna ci gaba da samun gagarumar nasara a yakin da suka fara kaddamarwa kan 'yan kungiyar Boko Haram da suke rayuwa a dajin Sambisa a matsayin babban sansaninsu.
Kanal Sani Usman ya kara da cewa: Sojojin na Nigeriya sun tsarkake kauyuka hudu daga mayakan kungiyar ta Boko Haram, kauyukan kuwa sune; Bala Karege, Goske, Harda da kuma Markas.
Har ila yau sojojin sun kwashi ganimar manyan makamai da kanana da kuma ababan hawa motoci da babura mallakin mayakan kungiyar ta Boko Haram.