Zargin Gwamnatin Ruwanda Da Hannu A Tashe-Tashen Hankulan Kasar Burundi
Gwamnatin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo ta yi zargin cewa: Kasar Ruwanda tana amfani da 'yan tawayen M23 na Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo da suka nemi mafaka a cikin kasarta wajen kara ruruta wutan rikicin kasar Burundi.
Kakakin gwamnatin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo Lambert Mende Omalanga a jawabin da ya gabatar a matsayin fadakar da kungiyoyin kasa da kasa kan rikicin kasar Burundi ya bayyana cewe: Gwamnatin Ruwanda tana da hannu a kara ruruta wutan rikicin kasar ta Burundi; Yana mai jaddada cewa: Mahukuntan Ruwanda suna amfani da kudade wajen amfani da mayakan kungiyar M23 da suka nemi mafaka a cikin kasashen Ruwanda da Uganda domin kara rura wutar masifar rikici da tashe-tashen hankula a Burundi da nufin kifar da gwamnatin kasar.
Kakakin gwamnatin Jamhuriyar ta Dimokaradiyyar Congo ya kara da fayyace cewa: Jami'an tsaron kasarsa suna kame 'yan tawayen kungiyar M23 da suke shigowa ta cikin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo domin shiga cikin kasar Burundi da nufin tada rikici da nufin kifar da gwamnatin kasar.