Matsalar Talauci Tana Kara Yin Kamari A Kasar Sudan
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i505-matsalar_talauci_tana_kara_yin_kamari_a_kasar_sudan
A wata sanarwa da Hukumar Kula Da Hakkokin Shari'a ta kasar Sudan ta fitar ta tabbatar da cewa matsalar talauci tana kara habaka a kasar, inda a halin yanzu ta haura kashi 46 cikin dari.
(last modified 2018-08-22T06:57:47+00:00 )
Feb 09, 2016 02:20 UTC
  • Matsalar Talauci Tana Kara Yin Kamari A Kasar Sudan

A wata sanarwa da Hukumar Kula Da Hakkokin Shari'a ta kasar Sudan ta fitar ta tabbatar da cewa matsalar talauci tana kara habaka a kasar, inda a halin yanzu ta haura kashi 46 cikin dari.

Shafin watsa labarai na Arrakuba a jiya Litinin ya nakalto daga babban jami'in Hukumar kula da hakkin shari'a na Zakkah a kasar Sudan Abdul-Halim Ali Sayyid yana cewa; Ba zai yiyu a samu nasarar shawo kan matsalar hauhauwa talauci a kasar Sudan ba cikin dan gajeren lokaci, domin a halin yanzu haka matsalar talaucin tana kara hauhauwa inda ta haura kashi 46 cikin dari.

Har ila yau a ganawarsa da gidan talabijin din Asshuruk Abdul-Halim Ali Sayyid ya bayyana cewa; Suna kokarin ganin a cikin wannan shekara ta 2016 sun samu nasarar kubutar da iyalai 30,000 daga kangin talauci, saboda suna tsammanin kudaden zakka da zasu tara zasu kai dalar Amurka miliyan 370, kuma zasu yi kokarin ganin raba kudaden ga iyalan da suke cikin mummunan kangin talauci a kasar.