Bukatar Bazata na Amnesty International ga Gwamnatin Najeria
Kungiyar Kare hakin bil-adama ta bukaci Gwamnatin Najeriya da ta kiyaye Hakin wadanda ake tsare da su kan zarkin su da alaka da kungiyar Boko Haram
Ƙungiyar kare haƙƙin bil Adama ta Amnesty International ta ce akalla mutane 149 ne, da suka hada da ƙananan yara, suka mutu a 2016, a barikin sojin Najeriya.
Amnesty ta ce mutanen sun mutu ne a yayin da suke a tsare a barikin sojojin Giwa dake garin Maiduguri da ke arewa maso gabashin ƙasar, inda hukumomi ke ci gaba da fafatawa da 'yan ƙungiyar Boko Haram.
A wani rahoto da ta fitar a wannan Laraba, ƙungiyar ta yi zargin cewa ana tsare da mutanen ne a cikin wani mummunan hali da kuma ƙuntatawa.
Rahoton ya ce akalla ƙananan yara 11 ne suka rasa rayukansu da suka hada da jarirai sakamakon cututtuka , yunwa ishirwa da kuma harbin bindiga.
har ila yau kungiyar ta yi kira ga gwamnatin Najeriya data gaggauta sakin wasu mutane 1,200 da ake tsare da su a barikin soji na Giwa dake birnin Maiduguri na jahar Borno sannan ta rufe barikin baki daya.
Baya ga hakan kungiyar ta yi zargin cewa ana tsare da mutanen ne a cikin wani mummunan hali da ya keta hakkin bil’adama.