An buda taron Tattalin Arzikin kasashen Duniya kan Afirka A Ruwanda
An buda taron Tattalin Arzikin kasashen Duniya a kan Afirka karo na 26 A Birnin Kigali na kasar Ruwanda
Taron da za a kwashe kwanaki uku ana gudanar da shi ya samu halartar 'yan kasuwa sama da dubu da 200 da suka fito daga kasashen Duniya kimanin 70 daga cikin su a kwai shugabanin kasashen Afirka guda 10, inda tuni aka fara tattaunawa kan yadda za ake gudanar da kasuwanci ta hanyar na'urorin zamani.
Wannan taro na gudana ne a yayin da farashin mafi yawan kayan da kasashen Afirka ke sayar wa ke ci gaba da faduwa a kasashen Duniya.
A cewar mista Oliver Cann kakakin zauren taron, tattalin arzikin kasashen na Afirka ya ragu idan aka kwatamta shi da na shekarar da ta gabata, domin haka wajibi ne kasashen na Afirka su sake samun sabin dibaru na bunkasa tattalin Arzikin kasashen su fasa dogara da albarkatun kalkashin kasa da suke sayarwa a kasuwanin kasashen Duniya.
Mista Oliver Cann ya kara da cewa taron na bana zai fi maida hankali kan bunkasa tattalin arzikin yankin bisa dogaro da ci gaban na'ura mai kokoluwa.