Bukatar Kungiyar Turai ga Najeria
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i5074-bukatar_kungiyar_turai_ga_najeria
Kwamitin kungiyar Tarayyar Turai ya Bukaci Najeriya da ta karbi 'yan kasar ta dake gudun hijra a kasashe Turai
(last modified 2018-08-22T06:58:15+00:00 )
May 11, 2016 12:52 UTC
  • Bukatar Kungiyar Turai ga Najeria

Kwamitin kungiyar Tarayyar Turai ya Bukaci Najeriya da ta karbi 'yan kasar ta dake gudun hijra a kasashe Turai

Kamfanin dillancin Labaran kasar Faransa ya habarta cewa a wannan Laraba, kwamitin kungiyar Tarayyar Turai ya fara tattaunawa da Magabatan Najeriya inda suka bayar da shawarar cewa magabatan na Najeria su amince da mayar da 'yan kasar su da suka shiga kasashen turai ba kan ka'ida ba gida.

Wannan bukata dai na zuwa ne a yayin da kasashen Turai ke ci gidan wani yanayi na matsalar kudi saboda yawan kwararen 'yan gudun hijra cikin kasashen na su .

A bangare guda Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya ce shi dai ba ya bukatar a ba shi hakuri, game da kalaman da Firayi Ministan Biritaniya David Cameron ya yi da ke cewa Najeriya na gaba-gaba cikin kasashen da cin hanci ya yi wa katutu.

Da ya ke magana a wani taro game da cin hanci da rashuwa a birnin Landan, shugaba Buharin ya ce shi abun da ke gaban sa shi ne mayar da hankali wajen kwato kadarorin kasarsa da aka boye a bankunan Biritaniya.

Mista Cameron dai ya yi kubutar bakin ne a yayin da ya ke tattaunawa da sarauniya Elizabeth, a yayin da ya ke ma ta bayanin karbar bakuntan kasashen da zasu halarci wani taron koli kan cin hanci da rashawa da za a gudanar ranar Alhamis a birnin Londan.