Tsanantar Talauci A Murtaniya
An bayyana cewa fiye da kaso 40% na al'ummar Murtaniya su ke fama da talauci.
A wani rahoto da kamfanin dillancin labarun Xinhua ya fitar, ya ambato manzon musamman na majalisar dinkin duniya akan hakkin bil'adama a kasar ta Murtaniya, Phillips Alston yana cewa; Kaso 44% na mazauna karkara a kudancin Murtaniya suna rayuwa cikin bakin talauci da wahalar rayuwa.
Jami'in majalisar dinkin duniyar ya kuma ce; matukar ba a fito da siyasar tattalin arziki ta raba arzikin kasa cikin adalci ba, to shakka babu za a sami rashin tabbaci da tsaro.
Bugu da kari, Alston ya yabawa gwamnatin kasar ta Murtaniya saboda koarin da ta ke yi na ci gaban kasa sai ya sake jaddada kira a gare ta da ta zage damtse.