WFP / PAM : Ana Fama Da Matsalar Karamcin Abinci A Kudancin Afirka
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i5113-wfp_pam_ana_fama_da_matsalar_karamcin_abinci_a_kudancin_afirka
Hukumar samar da abinci ta duniya ta kiyasta cewa kimanin mutane miliyan 32 ke fama da matsalar karamcin abinci a kudancin Afirka.
(last modified 2018-08-22T06:58:15+00:00 )
May 12, 2016 23:19 UTC
  • WFP / PAM : Ana Fama Da  Matsalar Karamcin Abinci A Kudancin Afirka

Hukumar samar da abinci ta duniya ta kiyasta cewa kimanin mutane miliyan 32 ke fama da matsalar karamcin abinci a kudancin Afirka.

Wannan dai a cewar hukumar ta WFP / PAM na da nasaba ne da matsalar fari mai tsanani da yankin na kudancin Afirka ke fama dashi yau kusan shekara biyu.

Hakan kuma a cewar M. Andrew Odero wani kwarare kan matsalar karamcin abinci na hukumar a yankin babban abin damuwa ne, kasancewar ko a kakar bara a fuskanci irin wannan matsala.

A saboda haka hukumar ta ce tana kuma bukatar tallafin $ miliyan 677 domin agazawa mutanen da wannan matsala ta shafa, wannan kuma a tsawan lokacin daya kama daga watan Afrilu na bana zuwa na watan Maris na shekara ta 2017 dake tafe.

Tuni dai wasu kasashen yankin da suka hada da Afirka ta kudu, Malawi da Zimbabuwe suka ayyana dokar ta baci a wasu sassan kasar saboda matsalar ta fari wace ta kasance mafi muni da ba'a taba ganin irin ta ba a sama da shekaru 30 da suka wuce.