Najeriya : Dan Kunar Bakin Wake Ya Kashe 'Yan Sanda Biyu A Maiduguri
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i5116-najeriya_dan_kunar_bakin_wake_ya_kashe_'yan_sanda_biyu_a_maiduguri
Rahotanni daga Najeriya na cewa wani dan kunar bakin wake ya kashe 'yan sanda biyu tare da jikkata wasu 18 a Maiduguri babban birnin jihar Borno dake a arewa maso gabashin kasar.
(last modified 2018-08-22T06:58:16+00:00 )
May 13, 2016 00:22 UTC
  • Najeriya : Dan Kunar Bakin Wake Ya Kashe 'Yan Sanda Biyu A Maiduguri

Rahotanni daga Najeriya na cewa wani dan kunar bakin wake ya kashe 'yan sanda biyu tare da jikkata wasu 18 a Maiduguri babban birnin jihar Borno dake a arewa maso gabashin kasar.

Wata sanarwa daga kakakin rundinar sojin kasar Sani Usman ta ce dan kunan bakin waken ya tayarda baman-baman da yayi jigida dasu a harabar sakatariyar gwamnati a daidai lokacin 'yan sanda ke kokarin hana shi kusa kai a cikin ginin.

ita ma a nata bangare hukumar kula da agajin gaggawa ta kasar wato NEMA ta tabbatar da adadin mutuwar mutane biyu, saidai a cewar ta adadin mutanen da suka jikkata zai kai 19 zuwa 24.

Wasu rahotanni na daban sun ce tuni kungiyar Boko haram ta dau alhakin kai harin da sabon sunan ta na kungiyar IS a yankin yammacin Afirka a wata sanarwa data wallafa a shafinta na internet.

Wannnan dai na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ke shirin gudanar da wani taro a ranar Asabar din nan kan yaki da kungiyar ta Boko haram.