Shugaban Kasar Faransa Fransua Holanda Ya Isa Abuja Na Tarayyar Nigeria
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i5176-shugaban_kasar_faransa_fransua_holanda_ya_isa_abuja_na_tarayyar_nigeria
Shugaban kasar Faransa Fransua Holand ya isa Abuja babban birnin tarayyar
(last modified 2018-08-22T06:58:16+00:00 )
May 14, 2016 05:02 UTC
  • Shugaban Kasar Faransa Fransua Holanda Ya Isa Abuja Na Tarayyar Nigeria

Shugaban kasar Faransa Fransua Holand ya isa Abuja babban birnin tarayyar

Shugaban kasar Faransa Fransua Holand ya isa Abuja babban birnin tarayyar Nigeria don halattan taron yankin na yaki da kungiyar yan ta'adda ta Boko Haram. Jaridar Le Figaro ta kasar Faransa ta bayyana cewa shugaba Holand ya isa Abuja ne a jiya jumma'a bayan wani gajeren zanga da yayi a kasar Afrika ta tsakiya inda ya gana da shugaba Faustin Archange Touadéra, suka kuma tattauna kan sake gina kasar da kuma ficewar sojojin Faransa daga kasar.

A ranar talata mai zuwa wato 17 ga watan mayu da muke ciki ne za'a gudanar da taron yaki da kungiyar yan ta'adda ta Boko Haram a Abuja, kuma ana saran wakilai daga kasashen Kamaru, Chadi, Niger, Britania da kuma Amurka ne zasu sami halattan taron.

Kungiyar Boko Haram dai ta afar ayyukan ta'addanci ne ton shekaru 6 da suka gabata kuma ya zuwa yanzu ta kashe dubban mutane a kasashen Nigeria da makobtanta.