Dambaruwar Siyasa Tana Ci Gaba Da Daukan Sabon Salo A Kasar Mauritaniya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i5185-dambaruwar_siyasa_tana_ci_gaba_da_daukan_sabon_salo_a_kasar_mauritaniya
Dambaruwar siyasa tana ci gaba da daukan sabon salo a kasar Mauritaniya musamman bayan furucin baya- bayan nan da shugaban kasar ya yi na neman rusa Majalisar Dattijan kasar.
(last modified 2018-08-22T06:58:16+00:00 )
May 14, 2016 06:14 UTC
  • Dambaruwar Siyasa Tana Ci Gaba Da Daukan Sabon Salo A Kasar Mauritaniya

Dambaruwar siyasa tana ci gaba da daukan sabon salo a kasar Mauritaniya musamman bayan furucin baya- bayan nan da shugaban kasar ya yi na neman rusa Majalisar Dattijan kasar.

Tun bayan da shugaban kasar Mauritaniya Mohammed Wuld Abdel- Aziz ya gabatar da bukatar gudanar da zaman tattaunawa tsakanin gwamnati da 'yan adawar kasar musamman kan batun neman rusa Majalisar Dattijan Mauritaniya saboda rashin ganin amfaninta, wata sabuwar dambaruwar siyasa ta sake kunno kai a kasar lamarin da ya janyo taron gangamin 'yan adawa a birnin Nouakchott fadar mulki kasar domin nuna rashin amincewarsu da shawarar shugaban kasar.

Har ila yau 'yan adawa sun koka kan yadda mahukuntan Mauritaniya suke daukan matakan tursasawa kan jam'iyyun siyasar kasar musamman matakin baya-bayan nan da gwamnatin Mauritaniya ta dauka na haramta wasu jam'iyyun adawa ciki har da jam'iyyar adawa ta Tawa'sil.