Shugaban Kasar Faransa Ya gana da Shugaba Muhammad Buhari A Nigeria
May 14, 2016 15:11 UTC
An yi ganawa a tsakanin shugabannin Najeriya da na kasar Faransa a Abuja.
Kamfanin Dillancin Labarun Faransa daga birnin tarayyar Najeriya Abuja, ya ce an yi ganawa a tsakanin shugaba Muhammadu Buhari, da shugaban Faransa Francois Hollande.
shugaban kasar ta Faransa dai ya isa Najeriya ne tun jiya juma'a domin halartar taron tsaro kasar wanda za a bude a ranar 17 ga watannan na Mayu. Taron dai zai sami halartar kasashen da su ke makwabta da Najeriya din da kuma wasu kasashen duniya.
Kungiyar Bokoharam wacce taron zai maida hankali wajen tattauna hatsarinta da kuma hanyoyin ci gaba da fada da ita, ta dauki shekaru tana a matsayin barazana ga kasar da makwabtanta.
Tags