Burkina Faso na shirin janye rabin sojojinta daga yankin Darfour
May 15, 2016 11:01 UTC
A wani mataki na kalubalantar barazanar ta'addanci a doron kasarta, Burkina Faso na shirin janye rabin sojojinta 850 dake yankin Darfour, a cewar ma'aikatar tsaron kasar.
Kasar Burkina Faso, kamar sauran kasashen shiyyar yammacin Afrika na fama da barazanar ta'addanci, don haka a cewar manjo janar na rundunar sojojin Burkina Faso, Pingrenoma Zagre, kasar na bukatar sojojin ta domin tunkarar matsalar ta'adanci dake addabar kasashen makoftanta dama ita kan ta.
Idan ana tune ko a tsakiyar watan Janairu wannan shekara, wani harin ta'addanci da kungiyar Al-Qaida reshen yankin Maghreb wato AQMI t akai a kasar yayi sanadiyyar mutuwar mutane kusan 30.
Tags