Yan Sanda Sun Tarwatsa Masu Zanga-Zangar Lumana A Kasar Kenya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i5263-yan_sanda_sun_tarwatsa_masu_zanga_zangar_lumana_a_kasar_kenya
Rundunar 'yan sandan Kenya ta yi amfani da iskar gas mai sanya hawaye wajen tarwatsa taron zanga-zangar al'umma a birnin Nairobi fadar mulkin kasar.
(last modified 2018-08-22T06:58:16+00:00 )
May 16, 2016 12:55 UTC
  • Yan Sanda Sun Tarwatsa Masu Zanga-Zangar Lumana A Kasar Kenya

Rundunar 'yan sandan Kenya ta yi amfani da iskar gas mai sanya hawaye wajen tarwatsa taron zanga-zangar al'umma a birnin Nairobi fadar mulkin kasar.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya watsa labarin cewa: A karo na uku a cikin wata guda al'umma a birnin Nairobi fadar mulkin kasar Kenya sun fito zanga-zangar lumana domin neman rusa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta kasar {CENA} kafin lokacin gudanar da zabuka a kasar, amma sun fuskanci mai da martani daga rundunar 'yan sandan kasar, inda suka tarwatsa masu zanga-zangar da iskar gas mai sanya hawaye.

Rahoton ya kara da cewa: Masu zanga-zangar lumanan sun nufi babban ofishin hukumar zanben na CENA ne domin gudanar da taron gangami kan jaddada neman bukatar rusa ma'aikatan hukumar da nufin maye su da wasu sabbin jami'ai.

Yan adawa a Kenya dai suna zargin cewa da hannun Hukumar zaben kasar ta CENI ake shirya magudin zabe a kasar lamarin da ke hanna 'yan adawa taka wata rawa a zabukan kasar.