An kame tsagerun Niger-Dalta masu fasa bututun Man A Najeriya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i5281-an_kame_tsagerun_niger_dalta_masu_fasa_bututun_man_a_najeriya
Rundunar sojin Najeriya ta kama wasu daga cikin tsagerun Niger Delta da ke fasa bututun man fetir a yankinsu.
(last modified 2018-08-22T06:58:17+00:00 )
May 17, 2016 01:13 UTC
  • An kame tsagerun Niger-Dalta masu fasa bututun Man A Najeriya

Rundunar sojin Najeriya ta kama wasu daga cikin tsagerun Niger Delta da ke fasa bututun man fetir a yankinsu.

Kakakin rundunar, Rabe Abubakar ya tabbatar da kama tsagerun na kungiyar Niger Delta Avengers da ake zargi da lalata bututun man, abinda ke rage yawan man da Najeriya ke samarwa zuwa ganga miliyan 1.65 daga miliyan 2.2 a kowace rana.

Mr. Rabe bai yi karin bayani ba game da adadin mutanen da suka kama yayin da suka zarge su da hannu wajen fasa bututun mai na kamfanin Chevron.

A makon da ya gabata ne, kungiyar tsagerun ta bukaci ilahirin kamfanonin mai da su fice daga yankin nan da karshen watan da muke ciki.

A ranar Asabar din data gabata ne, sakataren harkokin wajen Birtaniya, Philips Hammond ya ce, shugaba Muhammadu Buhari na bukatar nazari kan tushen rikicin Niger Delta, inda ya ce nuna karfin soji ba zai magance matsalar ba illa tsananta ta.