An dakile harin kungiyar Ashabab a tsakiyar kasar Somaliya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i5284-an_dakile_harin_kungiyar_ashabab_a_tsakiyar_kasar_somaliya
Dakarun tsaron kasar Somaliya tare da hadin gwiwar Dakarun tabbatar da sulhu na kungiyar Tarayyar Afirka sun samu nasarar dakile wani harin kungiyar Ashabab a kasar
(last modified 2018-08-22T06:58:17+00:00 )
May 17, 2016 01:15 UTC
  • An dakile harin kungiyar Ashabab a tsakiyar kasar Somaliya

Dakarun tsaron kasar Somaliya tare da hadin gwiwar Dakarun tabbatar da sulhu na kungiyar Tarayyar Afirka sun samu nasarar dakile wani harin kungiyar Ashabab a kasar

Kamfanin dillancin labaran Xin Huwa na kasar China ya nakalto wani Jami'in kasar Somaliya a jiya Litinin na cewa Dakarun tsaron kasar tare da hadin gwiwar Dakarun tabbatar da sulhu na kungiyar tarayyar Afirka wato AMISON sun fatattaki mayakan kungiyar ta'addancin nan ta Ashabab a yayin da suka kai hari kan barin soja na wani kauye dake yankin Hiran na tsakiyar kasar.

Jami'in ya ce a kwashi tsahon sa'o'i ana masayar wuta tsakanin Dakarun tsaron da mayakan na Ashabab inda daga bisani mayakan na Ashabab suka ja baya, kuma ya zuwa yanzu babu wani labari na asarar rayuka.

Jami'in ya kara da cewa Jami'an tsaron kasar Ethiopia ne kalkashin kungiyar AMISON ke tare da Sojojin Somaliya a wannan barikin Soja.

Jim kadan bayan wannan hari, kungiyar Ashabab ta dauki alhakin kai harin.