Kotu Ta Hana Kungiyoyin Kwadago Shiga Yajin Aiki A Nijeriya
Kotun masana’antu a Nijeriya ta hana kungiyoyin kwadago ta kasar (NLC) da kuma ta 'yan kasuwa da masana'antu (TUC) fara yajin aikin da suka yi barazanar farawa a gobe Laraba.
Rahotanni daga Nijeriyan sun ce hukuncin kotun ya biyo bayan maka kungiyoyin kwadagon a kotu da gwamnatin tarayyar Nijeriyan ta yi ne inda ta nemi kotu da ta haramta wa kungiyoyin shiga yajin aiki a gobe Laraba, 18 ga watan Mayu.
Yayin da ya ke shigar da karar a madadin gwamnatin tarayyar, ministan shari’a kuma antoni janar na kasar, Barista Abubakar Malami ya shaida wa kotun cewa yajin aikin zai gurgunta al’amura a duk fadin kasar; don haka kotun ta dauki wannan matsaya ta haramta yajin aikin.
Wasu rahotannin sun ce har ya zuwa yanzu dai gwamnatin tana ci gaba da tattaunawa da 'yan kungiyar kwadagon wajen ganin an cimma matsaya dangane da cire tallafin man fetur wanda ya sanya man fetur ya kai Naira 145 a kowace lita a kasar, abin da ya sanya kungiyoyin kwadagon barazanar shiga yajin aikin sai baba ta gani din har sai gwamnatin ta janye wannan kuduri nata.
A ranar Asabar ne kungiyoyin NLC da TUC suka bai wa gwamnatin tarayyar wa'adin kwanaki 4 da ta janye karin kudin man fetur da ta yi ko su tafi yajin aikin na sai baba ta gani.