Najeriya : An Samu Rabuwar Kawuna Kan Yajin Aiki
May 18, 2016 07:23 UTC
A Najeriya an samu rabuwa kawuna gameda yajin aikin gama gari da mayan kungiyoyin kwadigo na kasar suka kira yau Laraba domin kalubalantar kara farashin man fetur da gwamnatin kasar tayi.
Yayin da kungiyar NLC ta soma yajin aikin na sai- baba ta gani daga yau Laraba, ita kuwa kungiyar TUC ta ce zata jingine yajin aikin don kada ta sabawa umurnin kotu.
Wannan dai ya kawo rabuwa kawuna tsakanin jagoran kungiyar ta NLC Ayuba Wabba da kuma na TUC Bobboi Kaigama.
A jiya ne dai kotun sasanta rikicin ma'aikata ta kasar ta hana kungoyoyin shiga yajin aikin saboda abunda ta kira, hana kasar fadawa cikin halin ni iya-su..
Tags