Tunisiya Ta Karbin Bashin Bankin Duniya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i5350-tunisiya_ta_karbin_bashin_bankin_duniya
Bankin Duniya Ya Bai wa gwamnatin kasar Tunisya Bashin Dala Biliyan Biyar
(last modified 2018-08-22T06:58:17+00:00 )
May 18, 2016 15:04 UTC
  • Tunisiya Ta Karbin Bashin Bankin Duniya

Bankin Duniya Ya Bai wa gwamnatin kasar Tunisya Bashin Dala Biliyan Biyar

Kamfanin Dillancin Labarun faransa ya ambato cewa; Bankin duniya ya amince da ya bai wa gwmanatin kasar Tunisiya bashin kudin da su ka kai dalar Amurka biliyan biyar domin yi wa tattalin arzikin kasar kwaskwarima.

Rahoton ya kuma kara da cewa bada bashin da bakin duniyar ya yi ga kasar Tunisiya ya zo ne domin karfafa kasar ta farfado da tattalin arzikinta da kuma samarwa da matasa aikin yi.

Tattalin arzikin kasar Tunisiya dai ya sami koma baya ne, saboda matsalolin da ake samu a harkar yawon bude ido da ita ce ginshikinsa.