Zaman shekara na ofishin dake buga Alkur'ani a kasar Sudan.
An buda zaman shekara na Ofishin dake buga tare da Watsa Alkur'ani mai tsarki na kasashen Afirka wanda ake kira da Gidan Alkur'ani na Afirka a kasar Sudan
A yau Alkhamis ne aka buda zaman bisa jagorantar Nazar Sheikh Jaili Shekhul-Mukashifi ministan shiryarwa da wakafi na kasar Sudan tare kuma da tawagar kasashen musulinci a birnin Khartoum fadar milkin kasar.
Daga cikin kasashen da suka halarci taron a kwai tawagar Saudi-arabiya, Qatar, Kuweit, Masar, Turkiya da wasu kasashen Afirka.
A yayin buda wannan taro magabatan birnin Khartoum sun gabatar da rahoton aikin da a kayi na shekara dangane da bugawa tare watsa Alkur'ani mai tsarki a kasashen Afirka shekarar da ta gabata tare kuma da gabatar da tsare-tsaren shekara mai zuwa tare da kudaden da ake bukata,
Mahalata taron za su tattauna kan yadda za a bunkasa yawan Alkur'anin da ake bugawa tare da inganta shi ta hanyar amfani da na'urori na zamani.
Shi dai wannan gida na Alkur'ani na kasashen Afirka na a matsayin wata hedkota ta aikin alheri da aka kirkiro ta tun a shekarar 1994 a birnin Khartum na kasar Sudan da nufin hidma ga Alkur'ani mai tsarki tare da watsa shi ga milyoyin mutane a kasashen Duniya musaman ma a kasashen Afirka