An sake fasa wani bututun Gaz a yankin Niger-Dalta a Najeria
Tsagerun Niger-Dalta sun sake fasa wani bututun iskar Gaz na kamfanin ENI mallakin kasar Italiya a yankin.
Kamfanin dillancin Labaran kasar Faransa ya nakalto magabatan Najeriya a yau Alkhamis na cewa tsagerun Niger-Dalta sun sake fasa wani bututun isgar Gaz a yankin na Niger-Delta, lamarin da yayi sanadiyar ragowar man fetur din da kasar ke fitarwa a ko wata Rana da ganga dubu guda.
A cikin makunin da suka gabata tsagerun na Niger-Dalta sun tsananta kai farmaki kan kamfanonin Man fetur din na kasashen waje dake fitar da Man a kasar tare da jan kunan 'yan kasashen wajen su kwashe yana su yana su su fice daga cikin kasar, wannan Lamari dai ya janyo ga tattalin arzikin kasar, inda yanzu haka man da kasar ke fitarwa a ko wata rana ya ragu.
A nata bangare, Gwamnatin Najeriya ta sha alwashi masu mumunar wannan dabi'a inda ko makun da ya gabata Dakarun kasar suka sanar da kame wani gungu daga cikin tsagerun Niger-Daltan masu fasa bututun Man.