Za'a Binciki Gwamnatin Rikon Kwarya A CRA
May 20, 2016 05:48 UTC
-
Tsohuwar shugabar RCA, Catherine Samba Panza
A Jamhuriya Afirka ta tsakiya gwamnatin kasar ta ce za'a binciki yadda hukumomin wucin gadi suka aiwatar da mulkin su.
Gwamnatin kasar ta bayyana hakan a yayin zamen majalisar ministocinta na baya bayan, koda yake bata fayyace lokacin za'a soma shirin ba ko kuma fannonin da batun ya shafa ba.
Saidai tuni wasu rahotanni suke ce za'a tabo batun wani tallafin kudade miliyan 2,5 na dallar Amurka da kasar Angola ta baiwa kasar, wadanda bayanai suka nuna cewa basu shiga asusun gwamnatin ba a wacen lokacin.
Tags