Harin Ta'addanci A Wani Masallaci A Tanzania.
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i5572-harin_ta'addanci_a_wani_masallaci_a_tanzania.
Mutane 3 sun kwanta Dama Sanadin Harin Ta'addanci A Masallaci.
(last modified 2018-08-22T06:58:19+00:00 )
May 21, 2016 07:57 UTC
  • Harin Ta'addanci A Wani Masallaci A Tanzania.

Mutane 3 sun kwanta Dama Sanadin Harin Ta'addanci A Masallaci.

A kalla mutane uku ne su ka kwanta dama sanadiyyar harin ta'addanci da aka kai a masallacin garin Mowanza da ke arewa maso yammacin kasar Tanzania.

A yau asabar ne Cibiyar watsa labaru ta International Business Timer ta ambaci cewa an kai harin ne a masallcin na Rahmani, tare da kashe mutane 3 da su ka hada da limamin masallacin.

Majiyar ta ci gaba da cewa; mutane 15 ne su ka kai harin suna rufe da fusakunku, inda su ka bude wute akan masallata.

Kawo ya zuwa yanzu dai babu wata kungiya wacce ta dauki alhakin kai harin, sai dai ana zargin kungiyar Da'esh, ( Isis) da hannu.