An Tabbatar Da Bullar Cutar Zika A Cap-Vert
Hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO ta shelanta cewa, ofishin nazari na cibiyar nazarin Pasteur ta Faransa dake birnin Dakar na Senegal ya tabbatar da cewa, yanzu kwayoyin cutar Zika dake yaduwa a kasar Cape Verde, da wadanda ke bazuwa a nahiyar Amurka, irinsu daya ne.
wannan dai babban abun damuwa ne kasancewar yana tabbatar da yadda cutar ta yadu daga kudancin Amurka, har kuma gshi ta sallamo a Afirka a cewar babbar jami'ar hukumar ta WHO Matsidisio Moedi.
Dan haka kuma a cewar jami'ar ya kamata kasashen Afirka su zabura domin tabbatar cewa cutar bata yadu ba zuwa sauran kasashen nahiyar.
Bayanai sun nuna cewa watakila irin wadannan kwayoyin cuta sun yadu ne daga Brazil zuwa Afirka.
Wannan ne karo na farko da aka gano irin cutar Zika dake yaduwa a nahiyar Amurka a Afirka.
Darektar kungiyar WHO reshen Afrika ta bayyana cewa, kasashen Afirka za su sake yin nazari kan hadarun da suka shafi wannan cuta, domin kyautata shirinsu na shawo kan yaduwar cutar.
Haka kuma, jami'ar ta shawarci kasashen Afirka da su yi kokarin kashe sauro, domin rage hadarin kamuwa da wannan cuta mai hadasa nakasa ta karamin kai ga jinjiri tun yana cikin cikin mahaifiyarsa.
zuwa ranar takwas ga wtan Mayu nan mutane 7.557 ne aka kiyasta cewa ko sun kamu da cutar a kasar ta Cap-vert