Saliyo : Mutum Na Karshe Dake Jinyar Ebola Ya Warke
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i559-saliyo_mutum_na_karshe_dake_jinyar_ebola_ya_warke
Cutar Ebola ta sake bulla ne jim-kadan bayan da hukumar WHO ta ayyana kawo karshen ta a yammacin Afirka
(last modified 2018-08-22T06:57:47+00:00 )
Feb 10, 2016 08:25 UTC
  • jami\'an dake kula da masu cutar Ebola
    jami\'an dake kula da masu cutar Ebola

Cutar Ebola ta sake bulla ne jim-kadan bayan da hukumar WHO ta ayyana kawo karshen ta a yammacin Afirka

A kasar Saliyo Mata ta karshe dake jinyar cutar Ebola ta warke.

kamar yadda hukumomin kiwon lafiya kasar suka sanar an ce matar wacce 'yar uwa ce ga mata data mutu sanadin cutar a watan Janairu da ya gabata ta warke.

Hakan dai na nufin daga yanzu za'a sanya ido har na tsawon kwanaki 42 domin tabbatar da cewa an kawo karshen cutar a kasar ko kuma A'a.

Idan ana tune matar ta farko ta mutu ne sanadin cutar ta Ebola jim-kadan bayan da hukumar lafiya ta Duniya ta ayyana kawo karshen cutar a yammacin Afirka.