Jam’iyyar PDP ta kore Shugabanta na kasa Ali Modu Sheriff
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i5593-jam’iyyar_pdp_ta_kore_shugabanta_na_kasa_ali_modu_sheriff
Rahotanni daga najeriya na cewa Jam’iyyar PDP ta kore Shugabanta na kasa Ali Modu Sheriff.
(last modified 2018-08-22T06:58:19+00:00 )
May 21, 2016 14:37 UTC
  • Jam’iyyar PDP  ta kore Shugabanta na kasa Ali Modu Sheriff

Rahotanni daga najeriya na cewa Jam’iyyar PDP ta kore Shugabanta na kasa Ali Modu Sheriff.

Tuni dai babbar jam'iyya adawa ta kasar ta nada tsohon gwamnan Kaduna Ahmed Makarfi a matsayin shugaban rikon kwarya.

Jam’iyyar ta kuma nada tsohon gwamann Anambra Peter Obi a matsayin mukadashin sakataren Jam’iyyar.

A cewar Jam’iyyar ta dau wannan matakin ne domin shawon kan rigingimun da suka mamaye ta, inda sabbin shugabannin data nada yanzu zasu ja ragamar jam’iyyar zuwa tsawon watanni Uku nan gaba.

Jam’iyyar PDP wadda ta mulki Najeriya tsawon shekara 16, ta kasance ba ta da shugaba tun bayan da Adamu Mu’azu ya sauka daga mukaminsa cikin shekarar bara bayan an kammala zaben 2015.