Taron Shekara-Shekara Na Bankin Raya Afirka.
An Bude Taron Shekara-Shekara Na Bankin Raya Nahiyar Afirka A Kasar Zambia.
Radiyon Faransa na kasa da kasa, ya bada labarin cewa; Daya daga cikin muhimman batutuwan da za a tattauna a yayin taron bankin raya nahiyar Afirka da aka bude a kasar Zambia, shi ne fada da rashin abinci mai raya jiki.
A jiya litinin ne dai aka bude taron bankin raya Afirkan na shekara-shekara wanda kuma zai ci gaba a yau talata.
Da dama daga cikin shugabannin kasashen nahiyar Afirka suna halartar taron.
A wani rahoto da bankin ya fitar ya bayyana cewa rashin abinci mai gina jiki yana haddasawa nahiyar Afirkan asarar da ta kai ta dalar Amurka biliyan 25.
An kafa bankin raya nahiyar Afirka ne a 1964 da zummar fada da talauci da kuma taimakawa kasashen Afirkan su ci gaba.