Shugaban Sudan Ya Sauke Babban Hafsan Hafsoshin Sojojin Kasar
Shugaban kasar Sudan Umar Hasan al-Bashir ya sauke babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Laftanar Janar Mostafa Obeid inda ya maye gurbinsa da Laftanar Janar Emadeddine Mostafa Adawi, wani na kurkusa da shi sosai wanda kuma ya taka rawa wajen tattaunawar da gwamnatin kasar take da 'yan tawaye.
Kamfanin dillancin labaran Reuters ya jiyo kakakin sojojin Sudan din yana tabbatar da wannan sauyin da aka yi wa tsohon babban hafsan hafsoshin sojojin Laftanar Janar Mostafa Obeid, wanda ya rike wannan mukamin kasa da shekaru ukun da suka gabata.
Kakakin Sojin dai bai ba da wani dalili na wannan sauyin da aka yi ba, yana mai cewa hakan yana daga cikin ci gaba da kwaskwariman da shugaba Bashir din yake yi wa gwamnatin tasa ne. To sai dai wasu majiyoyi suna fadin cewa wannan sauyin yana da nasaba da gazawar da Janar din yayi ne wajen kawo karshen 'yan tawayen gabashin kasar ta Sudan.
Tun a farko-farkon wannan shekarar dai rikici mai tsanani ya sake barkewa a yankunan Darfur da Yankin Marra da ke yammacin kasar ta Sudan tsakanin dakarun 'yan tawayen da na gwamnati lamarin da ya ke ci gaba da barazana ga gwamnatin ta Al-Bashir.